Kulub din Bayern Munich kasar Jamus ya sanar a Lahadin nan cewar dan wasan gaba na kulub din Jerome Boateng zai dakatar da buga wasanni sakamakon wasu raunuka a cinyarsa.
Shidai Boateng ya gamu da tsautsayi ne a lokacin karawar da suka yi tsakanin kulub dinsa da Hamburg wanda aka tashi da ci 2 da 1.
Wannan al'amari yasa kulub din na Bayern zai cigaba da harkokin wasanni ba tare da dan wasan sa Jerome Boateng ba. Wannan rauni na Boateng ya kasance a matsayin komabaya ga Josep Guardiola wanda yayi rashin fitaccen dan wasan bayansa.
Jerome Boateng, ya tsawaita wa'adin kwantiraginsa har zuwa watan Yunin shekarar 2021, kuma ya shiga wasannin har 27 a kakar wasannin ta wannan karo.(Ahmad Fagam)