Madam Lagarde da take bayani a ranar Jumma'an nan ta ce daure bakin aljihu wajen kashe kudin, rarrabuwan tattalin arzikin da yawan ciniki tsakanin yankuna abu ne da ake bukata don azalzala farfadowar yankin da ya yi kasa sakamakon faduwan kudin mai da kuma barazanar tsaro musamman ma harin kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar Nigeriya.
Har ila yau ta ce harin na kungiyar ta Boko Haram ya shafi yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru da sauran kasashen dake makwabtaka da Tabkin Chadi kamar su Chadi, Niger da Nigeriyan ita kanta, don haka ya wargaza ayyukan tattalin arziki da kuma karkata kudaden da aka tanada ma samar da ababen more rayuwa zuwa ga tsaro.
Kungiyar kasashe 6 na CEMAC na yankin tsakiyar Afrika na fatan cimma hauhauwar tattalin arziki zuwa kashi 3.5% a shekarar bana, ko da yake har yanzu bai cimma matsayin da aka cimma ba a shekarun baya. Don haka shugabar hukumar ta IMF Madam Lagarde ta bukaci sauran kasashe mambobi da su zuba jari a ayyukan more rayuwa don a samu rage gibin da zai iya sa a fuskanci yanayi mai wahala da kuma karuwan ciniki tsakanin yankunan. (Fatimah Jibril)