Babbar jami'a a sashin binciken tattalin arzikin duniya na bankin Standard Chartered na Africa Razia Khan ta shaida ma manema labarai hakan a Nairobi cewar tun asali cinikayyar kasa da kasa ba ta taba zama wani mizanin na cigaban tattalin arziki a Afrika ba.
A cewar masaniyar tattalin arzikin, Sin tana da shirin ta na cigaba da hulda da Afrika cikin dogon lokaci ko da kuwa tattalin arzikin ya yi kasa.
Ta ce adadin cinikayya tsakanin Afrika da kasar ta Sin ana sa ran zai kai dala biliyan 300, kuma zuba jari kai tsaye a farkon watanni 6 na shekarar bara ya kai dala biliyan 1.19.
Jami'ar Bankin na Standard Chattered tace kasashen Afrika masu girman tattalin arziki su ne suka fi yawan al'umma, shi ya sa Najeriya da Habasha suke da mafi girman tattalin arziki a Afrika baki daya in ji ta.
Madam Khan ta ce gibin kudin da yawancin kasashen Afrika ke samu ya karu tun daga karshen rikicin tattalin arziki na duniya.
Kasashe na samun natsuwa game da yawan gibin da aka samu, kuma ana ganin hakan ya sa matakin basukan su ke tafiya. In ji ta tare da bayyana cewa akwai bambanci sosai tskanin kasashen nahiyar daban daban a fannin gamuwa da hadari sakamakon basukan da ake ciwo wa a waje.
Ban da haka kuma, kara karfin dalar Amurka ya saka biyan bashi da kudaden kasashen waje ya kara tsada ma wassu kasashe.(Fatimah Jibril)