in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Afirka zai bunkasa da kashi 4.4 cikin 100 a shekarar 2016
2016-01-27 10:11:28 cri

Wani rahoto da MDD ta fitar a birnin Addis Abba na kasar Habasha, ya yi hasashen bunkasuwar tattalin nahiyar Afirka da kaso 4.4 cikin 100 a wannan shekara, daga kaso 3.7 cikin 100 a shekarar da ta dagaba

Rahoton ya ce, abubuwan da suka taimaka ga samun wannan nasara, sun hada da karuwar bukatun cikin gida da kuma ingantuwar yanayin cinikayya da yadda gwamnatoci suka kara zuba jari, musamman a fannoni muhimman ababan more rayuwa.

A jawabinsa yayin taron manema labarai game da wannan taron, manajan darektan sashen tsara manofofin yanayin tattalin arziki a hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin nahiyar Afirka (UNECA) Adam Elhiraik ya bayyana cewa, nahiyar Afirka za ta iya daidaita matsalolin tattalin arzikinta yadda ya kamata.

Sai dai duk da ci gaban tattalin arzikin da ake samu a nahiyar, kasashe irinsu Sudan ta kudu da Burundi na fama da kwamacalar siyasa da rashin tabbas, yayin da a daya hannu kasashe irin su Kenya da Somaliya ke fama barazanar ayyukan ta'addanci.

Har ila yau rahoton ya ce, tasirin yaduwar cutar Ebola a kasashen Guinea da Liberiya da Saliyo, shi ma ya shafi hasashen da aka yi na bunkasuwar tattalin arzikin yankin, ko da ya ke kasashen Guinea da Liberiya sun koma kan ganiyarsu na samun ci gaba.

Rahoton ya kuma yi hasashen cewa, tattalin arzikin yankin tsakiyar Afirka zai bunkasa da kaso 4.3 cikin 100 a wannan shekara, wato karuwar sama da kaso 3.4 cikin 100 a shekarar da ta gabata. Haka kuma tattalin arzkin yankin arewacin nahiyar ta Afirka zai bunkasa da kaso 4.1 cikin 100 a wannan shekara daga kaso 3.6 cikin100 a shekarar 2015.

Sai dai rahoton ya karkare da cewa, koma bayan tattalin arzikin duniya da faduwar farashin mai a kasuwannin duniya na iya zama babbar barazana ga bunkasar tattalin arzikin nahiyar ta Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China