in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da John Kerry a birnin Beijing
2016-01-27 21:01:55 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da sakataren wajen Amurka John Kerry, da sanyin safiyar Larabar nan a Birnin Beijing.

Cikin jawabinsa yayin ganawar tasu, Mr. Wang ya ce kasar Sin na da burin zurfafa musayar ra'ayoyi da Amurka a dukkanin sassan da suka jibanci kasashen biyu, domin bunkasa fahimtar juna tsakanin su.

Ya ce a matsayin su na wakilan dindindin a kwamitin tsaron MDD, ya dace su hada gwiwa da juna, wajen cimma daidaito a kan muhimman batutuwa.

Daga nan sai ya yi kira ga sassan biyu, da su ci gaba da aiwatar da sakamakon da aka cimma, a yayin ziyarar aiki da shugaban Sin Xi Jinping ya kai Amurka cikin watan Satumbar da ya gabata, a wani mataki na dora dangantakar kasashen biyu kan turba ta gari.

A nasa bangare Mr. Kerry cewa yayi Sin da Amurka, sun cimma nasarar kulla sabuwar alaka mai cike da martaba juna kan wasu batutuwa, ciki hadda batun nukiliyar kasar Iran, da na sauyin yanayi, da na yanayin da kasar Afghanistan ke ciki, da ma yakin da aka sha da cutar Ebola.

John Kerry ya ce sassan biyu na kuma da wasu muhimman batutuwa da ya dace su dauki matakan warware su, kamar batun nukiliyar Koriya ta Arewa, da kuma batun tekun kudancin kasar Sin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China