in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da sakataren harkokin waje na Amurka
2016-01-27 21:42:47 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da sakataren harkokin waje na kasar Amurka John Kerry a yau Laraba a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar ta su, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, a shekarar da ta gabata, an samu muhimmin ci gaba ta fannin bunkasa hulda a tsakanin kasashen Sin da Amurka, inda har ya karbi goron gayyatar da shugaba Obama ya ba shi, na gudanar da ziyarar aiki a kasar ta Amurka, tare da samun nasara, kuma bangarorin biyu sun cimma daidaito a kan kara bunkasa dangantakar da ke tsakaninsu.

Har wa yau, shugaban ya ce, bunkasuwar huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta dace da moriyar sassan biyu, haka kuma buri ne na daukacin kasashen duniya, don haka, ya kamata a kiyaye wannan hulda.

A nasa bangare Mr. Kerry ya ce, huldar da ke tsakanin Amurka da Sin na da matukar muhimmanci, kuma shugaba Obama na fatan kara tuntubar juna tare da shugaba Xi, don kara ciyar da huldar da ke tsakanin kasashen biyu gaba, tare kuma da kiyaye hadin gwiwar sassan biyu a harkokin duniya. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China