in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kocin Barcelona ya lashe lambar gwarzon mai horas da 'yan wasa na 2015
2016-01-14 14:28:40 cri
Mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafar Barcelona Luis Enrique, ya lashe lambar yabo ta koci mafi kwarewa a shekarar 2015, lambar da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ke bayarwa a duk shekara, a yayin bikin karrama manyan masu ruwa da tsaki a fagen tamaula wato Ballon d'Or.

A bana Luis Enrique ya samu nasara kan abokan takarar sa Josep Guardiola da kuma Jorge Sampaoli.

Luis Enrique dan shekaru 45 da haihuwa, ya jagoranci kungiyar Barcelona inda ta dauki kofuna uku a kakar wasa daya, nasarar da ita ce makamanciyar ta ta biyu a tarihin kafuwar kungiyar.

A shekarar 2015 kofin Spanish Super Cup ne kadai Enrique bai samu damar dauka ba, amma duk da hakan ana yiwa kungiyar ta Barcelona da yake horaswa, kallon zakaran gwajin dafi a tsakanin kulaflikan Sifaniya, da ma na sauran sassan duniya baki daya.

Enrique tare da tallafin manyan 'yan wasan Barcelona kamar su Lionel Messi, da Luis Suarez da Neymar, sun cimma nasarar lashe wasanni har guda 50 a shekarar ta 2015.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China