Ma'aikahar harkokin wajen kasar Syria ta gabatar da wasika ga babban sakataren MDD da shugaban kwamitin sulhun majalisar game da hare-haren boma-bomai da aka kai ga birnin Damascus a ranar 31 ga watan Janairu, inda ta zargi kungiyar 'yan ta'adda wajen kawo cikas ga shawarwarin shimfida zaman lafiya ta hanyar kaddamar da hare haren.
Kamfanin dillancin labarun kasar Syria ya bada labarin cewa, ma'aikatar harkokin wajen Syria ta yi kira ga babban sakataren MDD da shugaban kwamitin sulhun majalisar da su yi Allah wadai da hare-haren boma-bomai da aka kai kan fararen hular Syria a wannan rana.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta jaddada a cikin wasikar cewa, game da batun yaki da ta'addanci, bai kamata a maida batun a matsayin siyasa ba, ko kuma a yi amfani da ma'auni biyu mabambanta kan batun, a maimakon haka, ya kamata a bi dokokin kasa da kasa, da kuma nuna goyon baya ga kokarin da gwamnatin kasar Syria ke yi wajen yaki da ta'addanci.
An samu jerin fashewar boma-bomai a jiya Lahadi a garin Sayyidah Zaynab dake kudancin birnin Damascus. An kiyasta cewa, hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 50, a yayin da mutane fiye da dari suka jikkata. Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin wannan hari.
A wannan rana kuma, Staffan de Mistura, manzon musamman mai kula da batun Sham na babban magatakardan MDD ya yi shawarwari tare da wakilan manyan kungiyoyin adawa na kasar Sham a birnin Geneva, domin yin musayar ra'ayi kan shawarwarin shimfida zaman lafiya da aka fara. An bude sabon zagayen shawarwarin shimfida zaman lafiya na kasar Sham a ranar 29 ga watan Janairu a birnin Geneva. (Lami)