Wannan sanarwa ta kara da cewa, bayan da dakarun gwamnatin kasar Sham suka dauki jerin matakan sa ido, bisa amintaccen bayanin da aka samu, an ce, dakarun sojan gwamnatin sun kai hari daga sama kan sansanin rundunar dakarun Islam, inda ba ma kawai aka hallaka Zahran Alloush ba, har ma da wassu jagora na dakaru masu dauke da makamai na Rachman da na Ahrar al-Sham wadanda suke nuna adawa da gwamnatin kasar ta yanzu.
Wannan sanarwa ta kuma jaddada cewa, dakarun gwamnatin Sham za su ci gaba da dakile kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi har sai an rushe su gaba daya. A waje daya kuma, wannan sanarwa ta yi kira ga dukkan masu dauke da makamai da su ajiye makamansu, su koma al'ummominsu na halal, sannan ana fatan su bayar da gudummawarsu wajen tsaron kasar, da kawar da ta'addanci daga kasar. (Sanusi Chen)