in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kawo karshen ayyukan taron kwamitin hadin gwiwa karo na hudu na dangantaka tsakanin Sin da Gabon
2016-01-31 12:36:55 cri
Ayyukan taron hadin gwiwa karo na hudu tsakanin Sin da Gabon sun kammala a ranar Jumma'a a birnin Libreville bisa goron gyayyatar Gabon zuwa ga kamfanonin Sin masu zaman kansu da su shiga kasar Gabon domin zuba jari.

Bangaren noma ya kasance a matsayin muhimmin bangare inda kasar Sin take son kawo kwarewarta. Kasar Gabon dake fatan rage shigo da kayayyakin abinci ta kaddamar a 'yan watannin da suka gabata da wani shirin Graine dake manufar kafa da zuba kudi ga kungiyoyin manoma bisa hasashen ingiza samar da albarkatun gona a kasar.

Bangaren kasar Sin ya bayyana damarsa na taimakawa shirin Graine tare da taimakon musanyar fasahohi.

Game da dangantakar kudi, bangaren kasar Sin ya amince da shirin ayyuka goma sha daya da suka samu rancen kudi da aka jimilta zuwa fiye da Sefa biliyan 8, kimanin RMB miliyan 800.

Haka zalika, kasashen biyu kuma na gudanar da dangantaka kasuwanci mai kyau, inda a shekarar 2014, musanyar kasuwanci tsakanin Libreville da Beijing ta karu zuwa dalar Amurka miliyan 400. Kasar Gabon tana fitar zuwa kasar Sin da gurbataccen man fetur, itace da ma'adinai. Kasar Sin kuma tana fitar zuwa Gabon da kayayyakin masana'antu da kayayyaki na manyan ayyukan ci gaba.

Dangantakar diplomasiyya tsakanin Gabon da Sin ta fara a ranar 20 ga watan Afrilun shekarar 1974. A tsawon shekaru 42 na abokantaka, kasar Sin ta gudanar da manyan ayyuka a kasar Gabon, tare da gina manyan gine gine da dama kamar filin wasanni na abokantaka tsakanin Sin da Gabon, cibiyar gidan talabijin na Gabon, majilasar dokoki da majalisar dattawa, asibitocin jama'a biyu, hanyoyi da kuma madatsar ruwa ta samar da wutar lantarki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China