Game da hakan, fadar shugaban kasar Gabon ta fidda wata sanarwa, wadda ta yi matukar nuna adawa da matakin 'yan sandan na Faransa. Sanarwar ta ce wannan matakin wulakanci ne ga daraktan, kuma ya haifar da babban lahani ga kasar ta Gabon, kasancewar Mr. Accrombessi ya isa kasar ta Faransa ne domin gudanar da wasu ayyuka.
A shekarar 2007 ne hukumar daukaka kara ta kananan hukumomin birnin Paris, ta fara bincike kan wata kwangila da darajar ta ta kai Euro miliyan 7, wadda aka daddale tsakanin ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan kasar Gabon, da wani kamfanin yin tufafin soji na Faransa a shekarar 2006. Game da hakan ne kuma 'yan sandan birnin na Paris suka cafke wani ma'aikacin kamfanin.
'Yan sanda na Faransa dai na zargin Accrombessi da cin babbar moriya daga waccan kwangila, tare da zargin sa da yin sama da fadin wasu kudade. A jiya Litinin ne kuma hukumar tsara dokokin Faransa ta bukaci Accrombessi da ya bayyana rawar da ya taka wajen daddale waccan yarjejeniya. (Bako)