in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Sin da Gabon sun taya juna murnar cika shekaru 40 da kulla dangantaka
2014-04-20 16:09:35 cri
Shuwagabannin kasashen Sin da Gabon sun taya juna murnar cika shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashensu.

Cikin sakonsa a ranar Lahadin nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, cikin shekaru 40 da kafa dangantakar kawance da kasar Gabon, al'ummomin sassan biyu sun karfafa dankon zumunci karkashin managarcin tsarin martaba juna, da tallafawa juna tare da hadin gwiwa mai ma'ana.

Shugaba Xi ya ci gaba da cewa, kasashen Sin da Gabon sun samu gagarumin ci gaba a wannan sabon karni da muke ciki, yayin da hadin gwiwarsu kuma ya haifarwa al'ummunsu riba mai tarin yawa. Yana fatan dorewar dangantakar kawance tsakanin Sin da Gabon ya dace da burin al'ummunsu, musamman kasancewar kasashen biyu na da buri iri daya na samar da bunkasa da kyautata rayuwar jama'a.

Shi ma a nasa sakon, shugaba Ali Bongo Ondimba na kasar Gabon, cewa ya yi alakar kasarsa da Sin ta samu managacin ci gaba cikin shekaru 40 da kafuwarta, duba da yadda Sin ta tallafawa Gabon a fannonin ci gaba, ta kuma kasance abokiyar hulda ta musamman wadda ta baiwa shirin bukasar Gabon cikakken goyon baya.

Daga nan sai shugaba Bongo ya bayyana gamsuwarsa da nagartar ayyukan da kamfanonin kasar Sin ke gudanarwa a Gabon. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China