Rahotanni daga kasar Burkina Faso na cewa, an dage zaben kananan hukomin kasar da aka shirya gudanarwa a karshen watan Janairu bayan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki.
Majalisar ministocin kasar ta bayyana a jiya cewa, yanzu za a gudanar da zaben kananan hukumomin a ranar 22 ga watan Mayun wannan shekara, bayan wata tattauna tsakanin mahukuntan kasar da hukumar zaben kasar mai zaman kanta da kuma masu ruwa da tsaki a harkar siyasar kasar.
Masu kada kuri'a sama da miliyan 5.5 ne ake sa ran za su kada kuri'unsu don zaben magadan gari da kansiloli a sama da yankuna 300 da ke fadin kasar.
Masu sa-ido a zaben sun bayyana cewa, za a jibge dubban jami'an tsaro don tabbatar da cewa, an gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba a kasar da ke fama da hare-haren ta'addanci.
Zaben kananan hukumomin kasar ta Burkina Faso yana muhimmanci ga makomar kasar ta fuskar tsarin demokuradiya, tun bayan boren da ya kawo karshen mulkin Blaise Compaore na tsawon shekaru 27 a kasar.(Ibrahim)