Da take bayyana alhinin ta game da aukuwar harin, shugabar kwamitin zartaswar kungiyar ta AU uwargida Nkosazana Dlamini Zuma, ta ce AU za ta ci gaba da baiwa Burkina Faso da al'ummar ta goyon bayan da ya dace. Ta ce kwamitin tana matukar Allah wadai da aukuwar wannan lamari na rashin imani, wadda ya salwantar da rayukan fararen hula da ma wasu jami'an tsaro.
Zuma ta kuma gabatar da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata. Ta ce harin na baya bayan nan na zuwa a daidai gabar da sabuwar gwamnatin kasar ta maye gurbin gwamnatin rikon kwarya, a wani mataki na wanzar da tsarin dimokaradiyya, da adalci, tare da hada kan 'yan kasar, da kuma tabbatar da ci gaban kasar da ma yankin baki daya.
Uwargida Zuma ta kuma bayyana muhimmancin hadin gwiwar kasa da kasa da na shiyya shiyya, game da yakin da ake yi da ayyukan ta'addanci a daukacin sassan nahiyar Afirka. Ta ce ya zama wajibi sassan masu ruwa da tsaki su hada karfi da karfe wajen cimma nasarar wannan yaki. (Saminu Alhassan)