Da yake gabatar da jawabi ga mahalarta gangamin, shugaban kasar Burkina Fason Christian Kabore, ya ce shi da gwamnatin sa, da daukacin 'yan kasar na mika sakon ta'aziyyar rasa rayuka, ga iyalai da 'yan uwan mamatan. Ya ce maharan ba su da wani buri, wanda ya wuce jefa tsoro da firgici a zukatan al'ummar kasar, tare da fatan ganin sun dakile irin ci gaban da kasar ke samu.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Juma'a 15 ga watan nan ne wasu mahara dauke da makamai suka aukawa wani Otel, da wani wurin shan Kofi dake birnin Ouagadouou, fadar mulkin kasar ta Burkina Faso, lamarin da ya sabbaba mutuwa da jikkatar mutane da dama, ciki hadda baki 'yan kasashen waje.