in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi alawadai da hare haren ta'addanci a Burkina Faso
2016-01-17 13:47:54 cri
Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon, ya yi alla wadai a ranar Asabar da harin ta'addancin da ya faru tsakanin ranar Jumma'a da Asabar a Ouagadougou, babban birnin kasar Burkina Faso, da ya hakala mutane 29.

A cewar sanarwar kakakinsa, mista Ban ya jaddada goyon bayan MDD ga Burkina Faso da ma shiyyar wajen yaki da ta'addanci.

Ya kuma gayyaci hukumomin kasar da su yi iyakacin kokarinsu na ganin an gurfanar da wadanda suka kai wannan hari gaban kotu.

Haka ma shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya yi alla wadai a ranar Asabar da harin da aka kai a birnin na Ouagadougou, inda ya bayyana a cikin wani sako zuwa ga takwaransa na Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore, cewar al'umma da gwamnatin Cote d 'Ivoire tare da shi sun yi alla wadai da wadannan ayyuka na rashin imani da suka tura Burkina Faso cikin tashin hankali.

Haka zalika, shugaban kungiyar ECOWAS a wannan karo kana shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya yi allawadai a ranar Asabar da wannan harin ta'addancin da aka kai a ginin Otel Splendid da dakin shan kofi da cin abinci na Cappuccino dake Ouagadougou, a cikin wata sanarwa.

Shugaba Macky Sall ya bayyana cewa wannan hari ne da aka kai kan wata kasa ta kungiyar ECOWAS da ma gamayyar kungiyar baki daya.

Mr. Macky Sall ya ce, wannan wata dama ce gare shi na yin jaddada cewa ya zama wajibi a hada karfi da karfe domin kawar da ta'addanci a shiyyar yammacin Afirka domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da zaman jituwa, daga karshe kuma a kara karfafa hadin kai wajen da yakin da muke da wannan annoba, da yin hadin kai tare da sauran gamayyar kasa da kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China