Harin ta'addancin Ouagadougou: Wani dan siyasar Nijar daga cikin wadanda aka tsare da su
Wani dan takarar zaben shugaban kasar Nijar na shekarar 2016, Adal Roubeid, an tsare shi jam kadan bayan harin ta'addancin da ya rafu a ranar 15 ga watan Janairu a birnin Ouagadougou, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan talatin da jikkata wasu kusan hamsin, cewar wasu majiyoyi masu tushe a ranar Laraba.
A cewar ministan harkokin wajen Burkina Faso, Alpha Barry, mutane da dama na daga cikin wadanda ake tsare dasu bisa bukatun bincike game da harin na Ouagadougou. (Maman Ada)