Jiya Asabar kwamitin sulhu na MDD ya bayar da sanarwa, inda ya yi tofin Allah tsine da babbar murya kan harin ta'addanci da ya faru daren Jumma'a 15 ga wata a Ouadagougou, babban birnin kasar Birkina Faso.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, kwamitin sulhu na mara wa Burkina Faso da sauran kasashen da ke yankin baya wajen yaki da ta'addanci. Kuma akwai bukata da a kokarta wajen yaki da ta'addanci da kuma tsattauran ra'ayi na tashin hankali. (Kande Gao)