in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta aika da tawagar sa ido a jamhuriyar Afrika ta tsakiya
2015-12-26 13:07:10 cri
Kungiyar tarayyar kasashen Afrika wato AU ta aike da tawagar sa ido a kan babban zaben da za'a yi a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Tawagar karkashin jagorancin Souleymane Ndane Ndiaye, tsohon firaministan kasar Senegal, yana dauke da 'yan sa ido 40 daga kasashe 18 na Afrika kamar yadda bayani daga cibiyar kungiyar da aka fitar ranar Jumma'a ya nuna.

Tawagar sa ido a kan babban zaben yana da alhakin duba ayyukan zaben, adalci da sahihancin zaben, in ji sanarwar.

Bayan kada kuri'an, tawagar za ta fitar da ainihin abin da ta fahimta ta kuma amince a kai game da tafiyar da zaben a lokacin taron manema labarai.

A karshen zaben gaba daya, tawagar za ta gabatar da sahihanin bayani a kan daukacin zaben, a cikin rahoton karshe wanda za'a gabatar ma mahukuntar kasar jamhuriyar Afrika ta tsakiya da kuma wallafa shi, in ji sanarwar.

Tun da farko dai a tsai da ranar Lahadin nan 27 ga wata a matsayin ranar babban zaben kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya kafin a canza shi zuwa ranar 30 ga watan nan har ila yau, in ji hukumar zaben kasar. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China