An sanya wannan mataki a sahun gaba a yayin wani zaman taro da ya tattara wakilai 120 daga bangaren gwamnatin Senegal, masu zaman kansu, fararen hula, ilimi da bincike, da abokan hulda, a karkashin kungiyar FAO.
A kasar Senegal, noma na kasancewa har yanzu wani bangaren dake samar da mafi yawan guraben aikin yi. Kana yana wakiltar kashi 70 cikin 100 na al'ummar dake noma, tare da samar da damammaki ta fuskar samar da ayyukan yi, a lokacin da matasa dubu 269 a kowace shekara suke shiga kasuwar aiki, inda kimanin kashi 57 cikin 100 suka fito daga yankunan karkara, in ji Vincent Martin, wakilin FAO a Senegal.
Jami'in ya tabbatar da cewa muradi na uku, wato rage talauci a yankunan karkara na FAO na maida hankali wajen bunkasa samar da damammaki ayyukan karkara masu kyau ga matasan karkara.
Haka kuma wannan aiki, a cewarsa, na bayyana muhimmancin da kungiyar FOA take bayar ga ci gaban matasa a matsayin wani ginshikin rage talauci da kuma kyautata tsaron abinci.
A nasa bangare, Amadou Lamine Dieng, darekta-janar na cibiyar bunkasa samar da ayyukan yi ga matasa ta kasa (ANPEJ), ya nuna cewa noma na zama a halin yanzu a matsayin wani muhimmin makami dake tasiri sosai wajen samar da ayyukan karkara masu kyau ga matasa da mata. (Maman Ada)