in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Me ya sa kasar Sin take janyo hankalin kwararrun 'yan wasan kwallon kafa na kasar Brazil
2016-01-14 14:27:15 cri

Yayin da Dario Conca ya sanar da niyyarsa ta komawa kulob din Guangzhou Evergrande na kasar Sin a shekarar 2011, labarin bai janyo hankalin masu sha'awar wasan kwallon kafa na kasashe daban daban sosai ba, tun da yawancinsu sun fi mai da hankali kan 'yan wasa da kuloflikan nahiyar Turai.

Amma bayan shekaru 5, yadda dan wasan kasar Argentina din ya sake sauya sheka daga kulob din Fluminense na kasar Brazil zuwa Shanghai SIPG, bisa kudin kwangila dalar Amurka miliyan 10, ya sheda saurin bunkasar tsarin gasar kwararru ta kuloflikan wasan kwallon kafa na kasar Sin wato 'Chinese Super League'.

Albashi dalar Amurka miliyan 12 a ko wace shekara da aka baiwa Conca, ya sanya shi zama dan wasan kwallon kafa mafiya yawan albashi na 3 a duniya, inda yake biye da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi. Duk da cewa Labarin bai zama mafi janyo hankalin mutane a jaridun kasashen duniya, amma ya sanya kulaflikan kasar ta Sin fara mai da hankali kan nahiyar Amurka ta Kudu, musamman ma kasar Brazil.

Bayan hakan ke kuma 'yan wasan kwallon kafan kasar Brazil da dama, suka fara bin sawun Conca, inda suke rika sauya sheka zuwa kasar Sin a kai a kai. Musamman ma a watannin da suka gabata, yawan 'yan wasan Brazil dake taka leda a kasar Sin na karuwa cikin saurin gaske.

Cikin 'yan wasan Brazil da suke tamaula a kasar Sin, da wadanda suke taba taka leda a kasar, akwai Diego Tardelli (Shandong Luneng), Robinho (Guangzhou Evergrande), Paulinho (Guangzhou Evergrande), Ricardo Goulart (Guangzhou Evergrande), Jadson (Tianjin Songjiang), Luis Fabiano (Tianjin Songjiang)da Renato Augusto (Beijing Guoan).

A cewar Diego Tardelli, dan wasan Brazil dake bugawa kulob din Shandong Luneng na kasar Sin wasa, irin albashi mai tsoka da kuloflikan kasar Sin suka samarwa ya sa ake tururuwar taka leda a kasar ta Sin. Yayin da yake hira da manema labaru, dan wasan ya ce, duk da cewa zai iya zama cikin masu goyon bayansa, tare da samun damar gogawa da kwararrun 'yan wasa, ya kuma kara kyautata fasahar wasan kwallon kafar sa idan yana a kasar Brazil, a hannu guda irin albashin da ake bashi a kasar Sin ya na da yawa, kuma ana biya kan lokaci. A cewarsa yana da shekaru 30 a duniya yanzu, don haka tilas ne ya shiryawa zaman rayuwarsa a nan gaba.

Cikin dukkanin kuloflikan wasan kwallon kafar kasar Brazil, Corinthians shi ne ya fi fama da matsalar kwashe masa kwararrun 'yan wasansa daga kuloflikan kasar Sin. Kulob din da ya lashe kambin gasar Serie A ta kasar Brazil a shekarar 2015, kuma ya rasa 'yan wasan sa Jadson da Renato Augusto a cikin watan da ya gabata, yayin da Alexandre Pato, Ralf, Elias da Cassio su ma suke shawarar karbar gayyatar da kuloflikan kasar Sin suka yi musu.

A hakika ba wai 'yan wasan kasar Brazil ne kadai suke sha'awar zuwa kasar Sin ba, har ma tsoffin koci masu horar da 'yan wasan kungiyar kasar Brazil, kamar Luiz Felipe Scolari, da Mano Menezes su ma suna nuna kwarewarsu yanzu haka a kasar Sin.

Menezes ya fara zama manaja na kulob din Shandong Luneng na kasar Sin a watan Disambar da ya wuce, wasu makwanni bayan da Scolari ya jagoranci Guangzhou Evergrande inda kulaf din ya sake zama zakara a gasar Super League ta kasar Sin, a karo na 5 a jere.

Dalilin da ya sa kuloflikan kasar Sin ke janyo hankalin karin kwararrun 'yan wasan kwallon kafa na sauran kasashe kuwa shi ne, saboda tsarin gasar Super League na kasar ya zama daya daga cikin tsare-tsaren gasannin wasan kwallon kafa mafiya muhimmanci a duniya, kuma matakan gyare-gyare ga harkar wasan kwallon kafa da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar bara sun fara tabbata sannu a hankali.

Matakan sun hada da raba hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin daga hukumar gwamnatin kasar, don baiwa kungiyar ikon cin gashin kanta a fannonin kudi da aikin kula da 'yan wasa.

Ban da haka kuma, wani babban matakin da aka dauka, shi ne sanya fasahar wasan kwallon kafa ta zama, a matsayin daya daga cikin darussan da tilas ne yaran kasar su koya a makaranta.

Haka zalika, duk wanda ke son zuba jari ga wani kulob din wasan kwallon kafa, to, za a rage masa harajin da ya kamata ya biya, lamarin da ya tabbatar da samun isassun jari ga kuloflikan kasar. Ga misali, mista Ma Yun, wanda ya mallaki babban kamfanin hada-hadar cinikayya ta shafin yanar gizo wato Alibaba, ya zuba kudin da ya kai dalar Amurka miliyan 192 ga kulob din Guangzhou Evergrande, a cikin watan da ya gabata don mallakar kashi 50% na hannayen jarin kungiyar.

Gyare-gyaren da ake gudanarwa sun kasance karkashin burin kasar, na sanya kuloflikan Sin, da kungiyoyin kwallon kafa na maza da mata dake kasar, taka rawar a-zo-a-gani a fagen wasan kwallon kafa na duniya. Hakika dai wadannan matakai sun yi amfani, ganin yadda kungiyoyin kasar ta Sin suka riga suka fara samun ci gaba.

Ga misali, kulob din Guangzhou Evergrande ya zama zakara karo 2 a gasanni 3 da suka gabata, na kwararrun kulflikan nahiyar Asiya, haka kuma ya kasance na 4 karo 2 a gasar fidda gwani, ta kwararrun kulflikan duniya da hukumar FIFA ta shirya duk a shekarar 2013, da kuma 2015.

A bangaren kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin kuma, kungiyar ta shiga zagayen kusa da na dab da karshe, a gasar cin kofin nahiyar Asiya da ta gudana a bara, inda kungiyar ta rasa damarta, ta ci gaba a hannun kungiyar kasar Australia, wadda daga karshe ta lashe kofin. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China