in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AWF ta ba da taimakon dala miliyan 10 domin yaki da farautar namun daji ba bisa doka ba
2014-12-05 11:00:00 cri

Wata kungiya mai zaman kanta a Afrika dake kare namun daji AWF ta sanar da cewa, za ta ba da taimakon da dalar Amurka miliyan goma domin gaggauta kawo karshen kisa kiyashin da ake yi wa namun daji a nahiyar Afrika.

Kungiyar AWF ta bayyana a ranar Alhamis cewa, wadannan kudade za su taimaka wajen kawo karshen fataucin namun daji da sauran albarkatun daji zuwa kasashen waje, da ma kawar da bukatun hauren giwa da kahon bauna dake karuwa. Wadannan kudade na kulawa da bukatun gaggawa za su taimakawa duk ayyukan da suka dace domin kare al'ummar giwaye, bauna da sauran namun daji, in ji darekta janar na kungiyar AWF, Patrick Bergin a cikin wata sanarwar da aka fitar a birnin Nairobi, tare da kara cewa, wannan taimako na dalar Amurka miliyan goma ya shafi tsawon shekaru uku na kungiyar AWF ya zo daidai da adadin kudin farko da Amurka da Sin, manyan kasashen duniya biyu mafi karfin tattalin arziki suka yi alkawarin baiwa.

Haka kuma wannan taimako zai tallafa wajen zuba kudi kan ayyukan yaki da fataucin kayayyakin da aka sarrafa daga namun daji, da kuma dakila hanyoyin bunkasa wannan sana'a, ta hanyar cafke masu farauta ba bisa doka ba da masu fatauci, har ma da karfafa wayar da kai a yankin Asiya, ta yadda za'a rage bukatun kayayyakin da suka hada hauren giwa da kahon bauna da sauransu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China