Adadin namun daji na kara raguwa sosai a wuraren da ake kiyaye su, da ma inda ba a kiyaye wa a Afrika, masu bincike daga manyan jami'u da cibiyoyi na duniya suka sanar.
Sauyin manyan filaye, kamun namun dajin ba bisa doka ba, sauyin yanayi, karuwan yawan jama'a, tafiyar da mulki, tsare-tsare, tattalin arziki, sauye-sauye na zamantakewar yau da kullum, da gasa tsakanin kiwon dabbobi duk sun taimaka wajen raguwar cikin sauri, in ji Dr. Joseph Ogutu, wani jagoran masu bincike na jami'ar Hohenheim, cibiyar kimiyyar tsirrai, dake Stuttgart na kasar Jamus a cikin wani rahota da aka fitar.
Jinsin da suka fi saurin raguwa su ne bauna, Impala, gwanki, dorinar ruwa, karakanda, da sauran manyan namun daji da suka ragu daga kashi 77 zuwa 99 a cikin 100.
Giwa ce kawai ta karu da kashi 115 a cikin 100, da kuma jimina kashi 216 a cikin 100 a gabashi da yammacin Kajialo, in ji Dr. Norman Owen-Smith na makarantar kimiyyar kula da dabbobi, tsirrai, da muhalli, a jami'ar Witwatersrand dake kasar Afrika ta Kudu.
Rarraba manyan namun daji ya fi yawa a tsakanin shekarar ta 1977-2011 musamman a kan rakumin daji, impala da wildbeest.
Masanan kimiyya sun dora laifin raguwar namun dajin a kan rashin isasshen ruwan sama, karuwan yawan al'umma, amfani da filaye da dai sauran su.
Rayuwan dabbobin nan gaba a kan filayen kiwo a Kenya ya rataya ne gaba daya a kan gudunmuwa daga mazauna wuraren wadanda suke iyakacin kokarin suna kyale dabbobin su shakata, duk da tsadan da hakan kan haifar masu. (Fatimah)