in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibia za ta kira ga jami'an tsaro domin yaki da farautar namun daji
2014-07-09 10:43:52 cri

Gwamnatin kasar Namibia na shirin tura sojojinta domin kare namun dajin kasar daga masu farauta ba bisa doka ba, in ji wata jaridar kasar.

Wani rukunin musammun na yaki da harbin namun daji ba bisa doka ba zai fara aiki a cikin watanni biyu masu zuwa, kuma rundunar sojojin kasar ita za ta kara yawaita ayyukanta a cikin kasar domin shirya damarar yaki da masu farautar bauna da giwa, in ji jaridar Namibian Sun da ta rawaito kalaman ministan muhalli da yawon bude ido, Uahekua Herunga.

Rundunar sojojin kasar da sauran jami'an tsaro, za'a jibge su domin yin sintiri a yankunan da suka fi fama da wannan matsala, kamar yankunan Kavango Est, Zambeze, Kunene da Erongo. Kasashen dake makwabtaka da kasar kamar Angola da Botswana, za'a sanar da su ba da jimawa ba kan wannan mataki na karfafa yin sintirin jami'an tsaro a kan iyakokin kasar Namibia, in ji mista Herunga. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China