Majiyar ta ce wata yarinya ce mai shekaru kusan 13 ta afka wani gida a Kolofata, wani gari dake makwabtaka da Nigeriya da kusan karfe 6 na safe agogon kasar kafin ta kwance bam din dake jikin ta, abin da ya hallaka kanta da wadansu guda 5, da dama kuma suka ji rauni.
Majiyar ta ce daga cikin mutanen da suka mumman rauni guda 5 suka sake mutuwa a asibiti abin da ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa kusan 11.
Har yanzu dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin harin.(Fatimah)