Dan wasan gaban Shanghai SIPG Asamoah Gyan, ya soki lamarin matakin da hukumar shirya wasannin kwallon kafa ta Afrika CAF tayi na damka kyautar fitaccen dan wasan Afrika na shekarar 2015 ga Pierre-Emerick Aubameyang dan kasar Gabon.
Shi dai Aubameyang, yayi galaba ne akan abokan karawarsa wato Yaya Toure na Cote d'Ivoire da mataimakin kyaftin na kungiyar Ghana Andre Ayew, wanda ya amshi kyautar a yayin wani gagarumin bikin da aka shirya a Abuja hedkwatar mulkin Najeriya wasu kwanaki da suka gabata
Ya dai samu nasarar ne, a yayin da ya samu kuri'u 146, wadanda koci masu horar da 'yan wasa da kyaftin kungiyoyin kwallon kafa na Afrika suka kada.
CAF ta sha suka bayan kammala bikin bada lambar yabon, mutum na farko daya soki lamarin shi ne Yaya Toure, wanda ya taba lashe wannan lambar kyauta har sau 4, ya bayyana CAF da cewar ta zama hukuma marar kangado, abar Allah wadai, wanda kimarta ta zube a fadin nahiyar.
A nashi bangaren,Gyan, wanda kiris ya rage ya samu nasarar lashe kyautar, shi ma ya kalubalanci CAF, duk da haka ya amince da cewar abokin hamayyar tasa Aubameyang ya taka rawar gani.(Ahmad Fagam)