in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci Karin kudade don fuskantar matsalar El Nino a kusurwar Afrika
2015-12-24 09:52:35 cri
Ofishin MDD mai kula da harkokin jin kai a ranar laraban nan ya sake mika bukatar ta na samun Karin kudade don inganta fasahar tinkarar fitinar yanayi na El nino a kusurwa nahiyar Afrika.

Pete Manfield, Shugaban ofishin a lokacin ganawa da manema labarai a Nairobin Kenya ya ce ana bukatar Karin kayayyaki domin taimaka ma al'umma a wannan shiyya su jure sakamaon fitinar ya nayin na el nino da zasu fuskanta.

El-Nino yana kara ruruta yanayin jin kai da ake fuskanta a shiyyar. A yanzu haka an yi kiyasin mutane miliyan 2 za su iya rasa muhallan su idan ruwan sama mai karfin gaske na wannan el ninon ya taho don haka ake bukatar gaggauta samun kudin kai dauki.

Ofishin na MDD a makon jiya yayi gargadin cewa ruwan sama mai karfin gaske na El-Nino zai kara munanta yanayin karancin abinci da barkewar cututtuka a wannan shiyya na kusurwar Afrika.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China