in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UEMOA ta amince da wani kundin shiyya domin taimakawa kananan masana'antu
2015-12-20 13:03:05 cri
Kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA) ta amince a ranar Jumma'a a birnin Lome na kasar Togo da wani kundin shiyya domin taimakawa kanana da matsakaitan masana'antu (PME) bayan kwashe kwanaki uku ana tattaunawa.

Amincewa da wannan kundi wani bangare ne na tsarin aiki domin bunkasa da zuba kudi ga kanana da matsakaitan masana'antu a cikin kungiyar UEMOA (PAPF-PME), wanda burin haka shi ne baiwa masana'atu damar samun wani yanayi mai kyau, ta yadda za su kara yin takara a cikin kungiyar. Haka kuma, haduwar ta Lome, ta taimaka wajen shimfida tsarin doka na bunkasa PME, matsayin masu ruwa da tsaki daban daban da kuma hanyoyin da za a bi da ma aiwatar da kundin.

Kundin na kunshe da kudurori 45 da aka rarraba su zuwa matakai 6, musammun ma kan tsarin doka na bunkasa PME, daga bangaren shiyya zuwa na cikin gida, matakan rakiya masu nasaba da samun kasuwannin gwamnati, haraji, kirkire-kirkire, bincike, shiga cikin kasuwannin hada hadar kudi da kuma taimakawa PME dake cikin matsala.

Haka kuma kundin ya yi hasashen kafa ko karfafa wasu hukumomin da suka kware da kuma hanyoyin musammun da za su taimakawa kananan PME samun tallafin kudi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China