Mai rikon mukamin masanin harkokin tattalin arziki na bankin kana jami'in da ya wallafa wannan rahoto Punam Chuhan-Pole,ya shaidawa manema labarai ta hoton bidiyo cewa, an yi hasashen cewa, ci gaban yankin baki daya zai kai kashi 4.4 a shekarar 2016 kana zai karu zuwa kashi 4.8 a shekarar 2017.
Bugu da kari, rahoton ya nuna cewa, ci gaban tattalin arzikin kasashen na Afirka da ke kudu da hadamar Sahara zai ci gaba da fuskantar matsala, sakamakon sabbin matsalolin da yanayin tattalin arzikin duniya ke fuskanta, lamarin da ke tilastawa gwamnatoci bullo da sabbin matakan yin gyare-gyare don magance matsalolin cikin gida da ka iya kawo cikas ga ci gaban tattalin ariki.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, zuba jari a sabbin bangaroirin makamashi, mayar da hankali ga batun fari da illar sa ga tashar samar da hasken wutar lantarki ta hanyar amfani da ruwa, yiwa kamfanonin raba wuta mallakar gwamnati gyaran fuska, bullo da sabbin matakan karfafawa sassa masu zaman kansu kwarin gwiwa za su taimaka wajen kara karfafa sashen makamashi.
Daga karshe rahoton ya yi nuni da cewa, gwamnatoci za su iya kara yawan kudaden shigan da suke samu ta hanyar karbar haraji da inganta dokokin biyan haraji, kuma muddin aka tallafawa wadannan matakai, gwamnati za ta inganta hanyoyin kashe kudaden jama'a har ma ta samu rara a cikin kasafin kudinta.(Ibrahim)