Hukumar kididdigar kasar Kenya ta bayyana jiya Labara, cewar tattalin arzikin kasar Kenya ya karu da kashi 5.8% daga watan Yuli zuwa Satumba a shekarar nan mai karewa daga kashi 5.2 a makamancin wannan lokaci a bara.
Ofishin kididdiga ta kasar ta ce karuwar ya biyo bayan karfin ayyukan da aka yi ne a bangaren gine-gine, aikin gona, kudi, inshore da sayar da kaya a sari.
Bangaren gine-gine na daga cikin wanda ya fi saurin cigaba bayan da ya karu da kashi 14.1% a cikin wadancan watanni uku idan aka kwatanta shi da kashi 8.8% da aka samu a bara.
Hukumar ta lura da cewar, an samu wannan karuwar tattalin arzikin ne sakamakon karuwar kudin da ake kara ma fannin gine-ginen.
A wannan lokacin, bangaren ayyukan noma ya samu cigaba da kashi 7.1% idan aka kwatanta shi da na shekarar bara mai kashi 6.8%.
Wannan karuwar ya biyo bayan yawan samar da muhimman hatsi da madarar shanu, sannan kuma da karuwar ruwan sama da aka samu, in ji hukumar.(Fatimah Jibril)