151217-Ayew-na-kasar-Ghana-ya-shiga-jerin-sunayen-yan-takarar-neman-lambar-yabo-na-fitattun-yan-wasan-kwallon-kafa-na-Afrika-zainab.m4a
|
A ranar Litinin din nan CAF ta fitar da sunayen mutane ukun da zasu shiga takarar, wadan da suka hada da Andre Ayew na Ghana/Swansea City, da Pierre-Emerick Aubameyang na kasar Gabon na kulub din Borussia Dortmund, sai kuma Yaya Toure dan kasar Cote d'Ivoire na kulub din Manchester City
An zabi wadan da suka yi nasarar shiga takarra ne bayan da wata tawagar kwararru na shugabannin kungiyoyin kwallon kafa na CAF suka kada kuri'a.
Fitattun 'yan wasan Afrika na wannan shekara da suke zaune a Afrikan sune Baghdad Boundjah (Algeria/Etoile du Sahel), da Mbwana Aly Samata (Tanzania/TP Mazembe) da kuma Robert Kidiaba (DR Congo/TP Mazembe).
Za'a bayyana wadan da suka samu nasarar ne a wajen taron Glo-CAF Awards Gala, wanda za'a gudanar a ranar 7 ga watan Janairun shekarar 2016 a Abuja helkwatar Najeriya.(Ahmad Fagam)