in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta sha kashi a hannun DRC a wasan farko na rukunin B
2016-01-18 15:23:36 cri
A wasan farko na gasar cin kofin kasashen Afirka na CHAN da aka bude a kasar Ruwanda, Habasha ta sha kashi hannun janhuriyar dimokaradiyyar Congo, inda aka tashi wasan na ranar Lahadi Congo na da kwallo 3 Habasha na nema.

An dai buga wasan na rukunin B ne a filin wasa na Huye dake kudancin kasar ta Ruwanda, kuma dan wasa janhuriyar dimokaradiyyar Congo, Guy Lisadisu ne ya fara jefa kwallon farko a zaren kungiyar Habasha jim kadan da take wasa, sai kuma kwallon Heritier Luvumbu cikin minti na 46, kafin kuma Meshack Elia ya ci wa janhuriyar dimokaradiyyar Congon kwallo ta uku a minti na 58. Dukkanin yunkuri da 'yan wasan Habasha suka yi na rama kwallayen da aka zura musu ya ci tura, sun kuma zubar da damammaki masu yawa kafin kaiwa ga karshen wasan.

'Yan wasan janhuriyar dimokaradiyyar Congo ne dai suka lashe kofin wannan gasa a shekarar 2009.

A kuma ranar Alhamis mai zuwa kungiyoyin biyu za su buga wasan su na biyu, inda Habasha za ta kece raini da Kamaru, ita kuma janhuriyar dimokaradiyyar Congo za ta kwashi 'yan kallo da kasar Angola.

Gasar CHAN dai hukumar wasan kwallon kafar Afirka ce ke shirya ta, ta na kuma kunshe ne da 'yan wasa dake buga tamaula a cikin nahiyar ta Afirka kadai, banda wadanda ke buga wasanni a wasu kulaflikan ketare.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China