in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kocin yan wasan Najeriya ya bayyana shirin kulub din na shida gasar cin kofi ta Afrika
2016-01-04 15:16:26 cri
Shugaban kungiyar wasan kwallon kafa na Najeriya Super Eagles Sunday Oliseh, ya bayyana shirin kungiyar na shiga gasar wasannin cin kofin na kasashen Afrika na shekarar 2016 a kasar Rwanda.

Hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta Najeriyar NFF, ta shedawa kamafanin dillancin labaran ksar Sin Xinhua a birnin Legas cewar, Kocin ya ayyana sunayen 'yan wasa 23 da zasu halarci gasar.

Sanarwar ta kara da cewar rukunin B na kungiyar wasan ta Super Eagles, tare da rakiyar tawagar kwararru sun tashi zuwa birnin Cape Town na Afrika ta kudu da yammacin ranar Asabar da gabata.

Tawagar 'yan wasan zasu halarci wani horo na musamman na tsawon kwanaki 10, kuma zasu gudanar da wasannin sada zumunta guda biyu tsakanin su da Angola da kuma Cote d' Ivoire, a ranakun 6 da kuna 11 ga wannan watan na Janairu.

NFF ta ce, tuni Oliseh ya isa Afrika ta kudu gabannin zuwn tagawar.

Kungiyar Super Eagles B ta Najeriya ta kammala zagaye na 3 a wasan cin kofin kasashen Afrika wanda aka gudanar a kasar Afrika ta kudu a shekarar 2014.

Kulub din na Eagles zai shiga rukunin C a wasan na bana tare da takwarorin sa da sukayi nasara a shekarar 2011 da suka hada da Tunisiya, da Jamhuriyar Nijer da kuma Guinea, a wasan da za'a buda a Nyamirambo, Kigali na kasar Ruwanda.

Zadai a gudnar da wasan ne daga tsakanin ranakun 16 ga watan Janairu zuwa 7 ga watan Fabrairu na wannan shekara.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China