in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Real Madrid ta sallami Benitez ta maye gurbinsa da Zidane
2016-01-06 10:17:25 cri
A ranar Litinin din nan kungiyar wasan kwallon kafa ta Real Madrid ta salami mai horas da 'yanwasan ta na farko Rafael Benitez, kasa da watanni ukun farko na kakar wasanni ta wannan karon, sannan kuma nan take ta maye gurbinsa da Zinedine Zidane.

An dai sallami Benitez ne, kasa da sa'oi 24 bayan da aka tashi kunnen doki da ci 2-2 tsakanin Kulub din da wani tsohon kulob dinsa na Valencia, sakamakon wanda a yanzu haka yasa kulub din yana matsayi na 3 a gasar BBVA Primera Liga. Kuma sun tashi da maki 4 suna bayan Atletico Madrid, sannan suna da maki 2 a bayan Barcelona, wacce keda kwallo a hannu.

An sallami Benitez ne bayan da Real Madrid tayi nasarar tsallakewa a wasan share fage domin shiga rukunin cin kofi gasar kwararru ta Champions League kuma tayi nasarar lashe wasanni 11 daga cikin wasannin su 18 , inda ta samu wasanni 4 ta barar da wasanninta 3, duk da kasancewar daya daga cikin wasannin data tafka hasarar cikin sa an tashi ne da ci 4 – 0 tsakaninta da abokiyar hamayyar ta Barcelona.

Shugaban kulub din, Florentino Perez, ya fito fili a baina jama'a yana nuna goyon bayansa ga Benitez, bayan wannan nasara, Perez ya sake jaddada goyon bayansa ga Benitez inda harma yayi hira da wata kafar watsa labarai a ranar 17 ga watan Disamba , to amma abin mamaki sai gashi bayan makonni biyu kachal an sallami Benitez.

Tsonon Kocin na Valencia, da Liverpool, da Chelsea, da Inter Milan da kuma Napoli boss, ya fara rike kambun zama kocin ne daga kulub din Real Madrid bayan komawarsa gida inda ya maye gurbin Carlo Ancelotti a a dai dai lokacin fara kakar wasanni ta lokacin zafi, a lokacin ne harma ya zubar da hawayen murna a lokacin kaddamar da shi a hukumance.

Dangane da yanayin halayyar sa wajen yin taka tsan tsan, da kuma salon da yake amfani dashi na tsara dabarun yin nasara a wasanni ta hanyar bibiyar kura kuran da aka tafka a baya da daukar darasi a cikin kura kuran, wannan salo nasa bai samu karbuwa ba daga bangaren wasu daga cikin fitattun 'yan wasa ba, duk da cewa akwai jita jitar da ake bazawa cewar ana samun takun saka ne, a tsakanin 'yan wasan da mai horas da 'yan wasan. Yan wasan sun hada da James Rodriguez, da Isco, Marcelo da kuma Cristiano Ronaldo.

Matakin da tsohon Kocin na Real Madrid ya dauka a lokacin wasannin cin kofin King's Cup knockout tournament, inda ya canza wani dan wasan ya maye gurbinsa da dan wasa Denis Cheryshev, wanda ake zargin baragurbin dan wasane, wannan mataki bai bai haifarwa Mista Benitez da mai ido ba, duk da cewar ba laifinsa bane.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China