in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi allah wadai da harin da aka kai a Jakarta na Indonesia
2016-01-15 13:49:16 cri
Jiya Alhamis 14 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya fidda wata sanarwa ta kafofin watsa labarai, inda ya yi allah wadai da harin boma-bomai da bindigogi da aka kai a babban birnin kasar Indonesia, Jakarta.

Cikin sanarwar, kwamitin ya nuna juyayi ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, ya kuma nuna fatan wadanda suka jikkata za su iya samun sauki cikin sauri, kana ya mika sakon ta'aziya ga gwamnati da jama'ar kasa ta Indonesia.

Bugu da kari, kwamitin sulhu na MDD ya jaddada cewa, ya kamata a gurfanar da wadanda suka shirya da kuma aikata laifuffukan ta'addanci gaban kuliya da sauri, haka kuma da wadanda suka samar da kudi da kuma nuna goyon baya ga harkokin ta'addanci. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China