in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla shida suka mutu sakamakon fashewar bom a birnin Jakarta na kasar Indonesia
2016-01-14 19:47:29 cri

Wasu boma-bomai sun tarwatse da safiyar yau Alhamis din nan a birnin Jakarta hedkwatar kasar Indonesia, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 6. 'Yan sandan kasar kuma sun yi musayar wuta da wasu masu fafutuka.

Shugaban kasar Joko Widodo ya yi matukar Allah wadai da wannan aiki na ta'addanci. Mista Joko ya kuma gabatar da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da kuma alhini ga wadanda suka jikkata.

Gidan telibijin na kasar ya ba da labari kai tsaye game da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa bam na farko ya fashe ne da karfe 11 saura minti 20 na safe, a bakin kofar cibiyar sayar da kayyaki ta Sarinah dake tsakiyar birnin na Jakarta. Jim kadan da hakan ne kuma bam na biyu ya fashe, a wata tashar 'yan sanda masu lura da ababen hawa dake dab da cibiyar.

Baya ga wadannan bama bamai biyu, rahotanni sun nuna cewa an sake samun wasu hare-haren Bam din a wasu karin wurare.

Ya zuwa yanzu dai ba a san ko su waye suka kaddamar da wannan ta'asa ba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China