Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar Mista Ikbal, ya ce wadanda suka aikata wannan ta'asa su biyu suma sun rasu, yayin da suka tada bam din da ke jikinsu, kana 'yan sanda sun harbe ragowar maharan uku.
Mista Ikbal ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, an cafke wasu dake da hannu a kaddamar da harin, baya ga harbe sauran daga cikin su, matakin da ya dawo da kwanciyar hankali a kasar.
A nasa bangare, kakakin babbar hukumar 'yan sandan kasar Mista Anton Charliyan, ya musanta aukuwar tashin boma-bomai masu yawa, inda ya ce an kai harin ne kawai kan cibiyar sayar da kayayyaki ta Sarinah, da tashar 'yan sanda masu lura da ababen hawa dake daf da ita.
Dadin dadawa, shugaban kasar Mista Joko Widodo, ya fidda wata sanarwa a wannan rana, yana mai bayyana harin da aka kai a matsayin aikin ta'addanci, sa'an nan ya yi kira ga bangarori daban-daban, da su kaucewa yada jita-jita, gabanin fitar da cikakken sakamakon binciken da ake gudanarwa a yanzu. (Amina)