Hong Lei ya ce, bisa bukatar kasar ta Indonesia, rukunin masana na hukumar lura da jiragen saman fasinja ta kasar Sin, tuni ya isa yankin tekun kasar, tare da na'urorin zamani, domin neman akwatin nadar bayanan jirgin, yayin da jirgin ruwan ceto mai lamba 101, dake yankin tekun Kudu na ma'aikatar sufurin Sin ya gaggauta tashi zuwa yankin tekun, dauke da na'urar laluben akwatin nadar bayanai, da na tarkacen jiragen saman.