in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban ki-moon ya yi Allah-wadai da harin da aka kai a Jakarta
2016-01-15 11:04:57 cri
Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yi Allah-wadai da hare-haren bama-bamai da na bindiga da aka kai a Jakarta, babban birnin kasar Indonesia. Ban Ki-moon wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kakakinsa ya rabawa manema labarai, ya ce bai ga dalilin kai wadannan hare-haren ta’addanci ba. Mr. Ban ya kuma mika sakonsa na ta’aziya ga iyalan mutanen da hare-haren suka rutsa da su, sannan ya yi fatan wadanda suka jikkata za su warke cikin hanzari, ya kuma bayyana goyon bayansa ga gwamnati da al’ummar kasar Indonesia a kokarin da suke na yaki da ta’addanci. Ban Ki-moon ya kuma yi fatan za a zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aiki don ganin an hukuntasu. Rundunar ‘yan sandan kasar Indosesia dai ta dora alhakin harin na jiya Alhamis, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7, kana wasu 20 kuma suka jikkata kan kungiyar IS, duk da cewa, kungiyar ba ta saba kai irin wadannan hare-hare a yankin kudu maso gabashin Asiya ba. Amma bayanai na nuna cewa, yanzu haka kungiyar ta fara bude rassanta a kasashe daban-faban, ciki har da yankin kudu maso gabashin Asiya.(Ibrahim)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China