Yawan adadin wasannin tsere na gudun famfalaki da hukumar shirya wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta kasar Sin, CAA ta gudanar a shekarar 2015 ya karu zuwa 134, wanda ya karu da kashi 160 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2014.
Mataimakin shugaban CAA Du Zhaocai, shi ne ya sanar da hakan a kwanakin baya a nan birnin Beijing.
Du, ya fada a yayin taron Marathon a kasar Sin cewar, jimillar wasannin ya kai 134 wanda ya hada da wasannin gudun famfalaki wato marathons 53, da half marathons 43, da wasan tsere na tsawon kilomita 10 kimainin 13, sai kuma wasan tsere na kan titi kimanin 83 wanda ya zarta na shekarar 2014, sannan wasannin ya janyo hankalin baki kimanin miliyan 1 da dubu 500 daga kasashe daban daban kimanin 90.
A shekarar 2010, duka-duka wasannin marathons 13 ne aka karbi bakuncin su a kasar, adadin wanda ya nunka sau 10 yanzu, inji mista Du.
Du, ya kara da cewar, a yanzu hakan wasan marathon ya kasance wasa mafi shahara a kasar Sin wanda ke taimakawa wajen inganta lafiyar jama'a.(Ahmad Fagam)