in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yammacin Afrika na kan hanyar zama mara cutar ebola gaba daya
2016-01-14 10:16:44 cri
An sa rana kasar Liberiya zata bi sahun kasashen Saliyo da Guinea a yau alhamis na zama kasa na uku kuma na karshe a yammacin Afrika da zasu zama basu dauke da cutar ebola gaba daya, inji magatakardar MDD Ban Ki –Moon.

Da yake bayani a taron babban zauren majalissar game da cutar ebola da aka yi a jiya laraba ya ce sauran kwana daya kawai ya rage Liberiya ta fada sahun kasashen da basu dauke da cutar a karon farko tun barkewar ta.

Sai dai kuma Mr Ban yayi kiran da a ci gaba da sa ido sosai yana mai lura da cewar Liberiyan ta riga ta samu sake bullowar cutar har sau biyu kuma kasashen da abin ya shafa a shirye suke na kara farfado da shirin su na ko ta kwana domin dakile kwayoyin cutar.

Magatakardar MDD ya kuma yi kira da a cigaba da bada kula na jinya da goyon baya ga fiye da mutane 10,000 da suka tsira daga cutar ta Ebola a yammacin Afrika baki daya wadanda da daman su suka yi ta shiga cikin wani halin kunci.

Mr Ban Ki-Moon sannan ya yaba ma taimakon gaggawa da kasashen duniya suka bayar lokacin barkewar annobar tare da jinjina ma karfin halin ma'aikatan jinya da tawagar masu rufe gawawwaki.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bada rahoton cewa a kalla mutaen 28,637 ne suka harbu da cutar ta ebola kuma daga cikin su guda 11,315 sun mutu musamman a kasashen Guinea,Liberiya da Saliyo a lokacin da annobar ta barke a shekara ta 2014.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China