in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka sun bayyana kudurinsu na aiwatar da yarjejeniyar TFA da aka cimma
2015-12-17 10:22:34 cri

Kasashen Afirka da ke yankin kudu da hamadar Sahara sun bayyana kudurinsu na ganin sun aiwatar da yarjejeniyar harkokin cinikayya ko TFA a takaice da aka cimma.

Manyan jami'an kwastan na kasashen Afirka sun bayyana cewa, yarjejeniyar za ta taimaka wajen bunkasa harkokin cinikayya da zuba jari a nahiyar ta Afirka.

A jawabin da ya gabatar yayin wani taro da hukumar tara kudaden shiga ta kasar Kenya da kungiyar kwastan ta duniya ta shirya a gefen taron ministoci na kungiyar WTO karo na 10 da ke gudana yanzu haka a birnin Nairobin kasar Kenya, kwamishinan hukumar tara kudaden shiga ta kasar Kenya John Njiraini, ya bayyana cewa, sanya hannun kan yarjejeniyar ta TFA za ta baiwa kasashen Afirka damar kara amfana da harkokin cinikayya da zuba jari.

Bayanai na nuna cewa, a shekarun biyun da suka gabata hukumomin kwastan na nahiyar Afirka sun zuba jari a bangaren fasahohin zamani da horar da ma'aikata ta yadda za su inganta ayyukansu na kula da kan iyakoki da safarar kayayyaki da harkokin cinikayya cikin sauki.

Darektan kula da hadin gwiwar shiyya da sashen ciniyayya na bankin raya Afirka Moono Mupotola ya ce, hanya daya tilo ta hanzarta aiwatar da wannan yarjejeniya ita ce, hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci da sassa masu zaman kansu.

Don haka ya ce, wajibi ne hukumomin kwastan na kasashen Afirka da sassan masu zaman kansu su hada kai don ganin an aiwatar da yarjejeniyar TFA da za ta kasance mai fa'ida ga sassan biyu a bangaren tara kudaden shiga da saukaka harkokin kasuwanci.

Kimanin kasashen Afirka 30 ne suka sanya hannun kan yarjejeniyar ta TFA, tun lokacin da aka gabatar da ita yayin taron kungiyar WTO na farko da ya gudana a kasar Indonesia a watan Disamban shekara 2013.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China