Bayanan dake kunshe cikin takardar sun waiwayi tare da tattara fasahohin da aka samu, wajen raya dangantaka tsakanin Sin da kasashen Larabawa, tare da bayyana ka'idar bunkasa dangantaka tsakanin sassan biyu, sa'an nan ta tsara fasalin hadin gwiwa irin na cimma moriyar juna tsakaninsu, da kuma nanata burin gwamnatin kasar na ganin an tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta tsakiya, a kokarin sa kaimi ga daukaka dangantaka tsakanin Sin da kasashen Larabawa zuwa wani sabon mataki.(Fatima)