in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron ministoci karo na shida na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Larabawa
2014-06-05 20:48:36 cri

Yau Laraba 5 ga wata, a nan Beijing ne aka rufe taron ministoci karo na shida na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa.

Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, muhimmin jawabin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi a yayin bikin bude taron ya tabbatar da muhimman fannoni da kasashen Sin da Larabawa za su mai da hankali a kai wajen yin hadin gwiwa a tsakaninsu a shekaru 10 masu zuwa, inda kuma ya gabatar da wasu sabbin matakai da manufofi wajen yin hadin gwiwa. Jawabinsa zai yi jagora kan yadda bangarorin 2 za su bunkasa huldar da ke tsakaninsu a nan gaba. Kasar Sin na son hada kai da kasashen Larabawa wajen aiwatar da ra'ayi daya da aka cimma a yayin taron, a kokarin kawo wa jama'ar Sin da Larabawa alheri.

Wakilan kasashen Larabawa sun nuna cewa, shawarar da shugaba Xi Jinping ya bayar za ta raya huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Larabawa zuwa sabon matsayi, da amfanawa wajen samun bunkasuwa mai dorewa da zaman lafiya a kasashen Larabawa da Sin da ma duk duniya baki daya. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China