in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barcelona ta lashe kofuna 5
2015-12-23 15:25:48 cri
Yanzu haka dai kungiyar kwallon kafar Sifaniya wato Barcelona, ta lashe kofuna 5 a bana, bayan da a ranar Lahadi ta dauki kofin manyan kulaflika da hukumar FIFA ke shiryawa, a wasan karshe da suka buga da River Plate.

Messi ne ya bude ragar River Plate a minti na 34 da take kwallo. Sai kuma kwallaye biyu daga Luis Suarez. Haka kuma aka tashi wasan Barcelona na da kwallo 3 River Plate na nema.

Kafin wannan nasara dai Barcelona ta lashe kofunan Spanish league, da Copa del Rey, da na zakarun Turai, da kuma UEFA Super Cup.

Game da wannan nasara da kungiyar ta samu, kocin ta Luis Enrique, ya bayyana farin cikin sa, yana mai cewa sun cimma burin su, kuma suna matukar alfahari da hakan.

Suarez na Barcelona ya ci kwallaye 5 a wasannin 2, wanda hakan ya bashi damar lashe takalmin zinari na gasar ta manyan kulaflika da hukumar FIFA ke shiryawa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China