Babban jami'in kulub din na Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge, ya tabbatar da cewa Guardiola, ba zai sake sabunta kwantiraginsa da kulub din ba, wacce za ta kare a watan Yunin shekarar 2016. A sakamakon hakan shugabannin Bundesliga sun amince da Carlo Ancelotti ya maye gurbin sa. Mai horas da 'yan wasan dan shekaru 56 dan kasar Italiya, shi ne ya rattaba hannu a kan kwantiragin na tsawon shekaru 3, wanda zata fara a 2016 a lokacin hunturu.
Rummenigge ya sanar a shafin internet na kulub cewar, sun yabawa Pep Guardiola, bisa irin gudumowar da ya baiwa kulub din tun daga shekarar 2013. Sannan ya bukaci dukkannin tawagar kulob din dasu rubanya kokarin su domin cike gibin Pep, wanda yake shirin bankwana da kulub din.
Tsohon kocin na Barcelona, ya fara aiki da Bavarian ne a shekarar 2013 bayan ya rattaba hannu wanda zai kare a watan Yunin shekarar 2016.
Sai dai kuma Guardiola, har yanzu yana da wata damar na lashe gasar kwararru ta UEFA da kuma na German Cup da Bundesliga a kakar wasannin ta wannan lokaci.