in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron tunawa da cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kin harin Japan a kasar Senegal
2015-08-23 14:28:14 cri

Kungiyar sada zumunci tsakanin Sinawa kana kungiyar sa kaimi ga samun zaman lafiya da dinkuwar kasa ta kasar Sin da ke Senegal ta kira taron tunawa da cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kin harin Japan a Dakar hedkwatar kasar Senegal a ran 22 ga wata. Jakadan Sin dake kasar Xia Huang shugaban kungiyar Li Jicai, wakilan hukumomin Sin, da Sinawa dake Senegal kimanin 100 sun halarci taron.

Mista Xia Huang a cikin jawabinsa ya nuna cewa, an waiwayi tarihi a yayin taron ne domin koyon darasi daga wajen wannan yaki da kuma hana sake abkuwarsa, a maimakon ci gaba da sanya kiyayya. Jama'ar Sin da Afrika, dukkansu sun sha wahalhalu sakamakon yake-yake, saboda haka, suna mai da muhimmanci sosai kan zaman lafiya da zarafin samun bunkasuwa da suke samu yanzu. Hakan ya sa, Sin da kasashen Afrika suna daukar nauyi iri daya bisa wuyansu, wato yin amfani da wannan zarafi mai kyau wajen samun wadatar kasa da farfadowar al'umominsu.

A nashi bangare, Mista Li Jicai ya ce, al'ummar Sinawa da dama sun sadaukar da rayukansu don samun nasarar yakin kin harin Japan, da kuma kare ikon mulkin kasa da cikakken yankin kasar Sin. An gudanar da wannan taro mai jigon "Tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japan" ne da zummar tunawa da jaruman da suka sadaukar da rayukansu a lokacin yakin, domin kada a manta da wannan tarihi, da kuma yin kira ga mutane da su nace wajen samun zaman lafiya, da kishin kasa, da farfado da kasar Sin yadda ya kamata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China