Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta shaidawa taron manema labarai yau a birnin Beijing cewa, kasar Sin tana mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa game da batun, kuma tana fatan lamarin ba zai kai ga barkewar rikici ba.
Ta ce, kasar Sin tana fatan bangarorin biyu za su warware takaddamar da ke tsakaninsu ta hanyar shawarwari da tuntubar juna, a kokarin ganin an samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar.
Bayanan na Madam Hua na zuwa ne bayan da kasar Saudiya ta sanar da katse huldar diflomasiya da kasar Iran, sannan ta bukaci jami'an ofishin jakadancin kasar da ke Saudiyya da su fice daga kasar cikin sa'o'i 48.
Idan ba a manta ba a ranar Asabar ne wasu Iraniyawa masu zanga-zanga suka kona ofishin jakadancin kasar Saudiya da ke Tehran, domin nuna bacin ransa kan hukuncin da kasar saudiyya ta yanke na rataye wasu Iraniyawa 47 bisa zarginsu da aikata ta'addanci. (Ibrahim Yaya)