A wata sanarwa dauke da sa hannun mista Ban, mai Magana da yawun babban sakataren ta ce, Ban ya yi amanna cewar, ta hanyar tattaunawa ne kadai za'a warware rikicin kasar, da kuma tabbatar da samun fahimtar juna a tsakanin alummomin kasar ta Yemen, bayan fuskantar yakin basasa na tsawon watanni wanda ya yi sanadiyyar lakume rayukan dubban jama'a a kasar.
Kazalika Ban, ya yi maraba da matakin da bangarorin da ba sa ga maciji da juna a kasar suka dauka, na yin alkawarin tsakaita wuta a yayin da ake shirin kaddamar da tattaunawar.
Sannan ya bukaci dukkannin bangarorin kasar da su mutunta wannan yarjejejniyar, domin gudanar da ayyukan da za su tabbatar da samun dawwamamman zaman lafiya a kasar.
Bugu da kari, babban sakataren, ya bayyana kyakkyawar fatarsa na cewar tattaunawar zata kawo karshen rikicin sojin a Yemen, kuma zata sanya kasar kan turbar zaman lafiya mai dorewa.
Sannan ya yi kira ga bangarorin kasar da su kai zuciya nesa , kuma su amince wajen aiwatar da matakan da zasu kawo karshen mawuyacin halin da al'ummar kasar ke ciki, domin jama'a su samu damar gudanar da al'amuran su na yau da kullum.(Ahmad Fagam)