Babban bankin kasar ta Sin ya kuma tsaida kudurin karfafa ayyukan hukumomin hada-hadar kudi a fannin daidaita tsari, da kara goyon bayan kananan kamfanoni, da aikin gona, da manyan ayyukan samar da wutar lantarki ta karfin ruwa.
Wannan sabon kuduri na rage yawan kudin da ake ajiyewa da ya shafi cibiyoyin bada rance na kauyuka, da bankunan garuruwa, da sauran hukumomin hada-hadar kudi na kauyuka da kashi 1 cikin dari, zai kuma kunshi bankunan raya kauyuka na kasar ta Sin, wadanda za su rage kashi 2 cikin dari.
Ban da wannan kuma, babban bankin ya tsaida kudurin kara rage yawan kudin da ake ajiyewa ga bankunan kasar, da na ciniki na kasar, wanda hakan ya dace da sharadi, da yawan rancen kudin da suke samarwa kananan kamfanoni, da fannin aikin gona wanda ya wuce alkalamin da aka tsara da kashi 0.5 cikin dari bisa na sauran hukumomin hada-hadar kudi na kasar.
Wannan ne karo na biyu da babban bankin ya sanar da rage yawan kudin da ake ajiyewa, bayan da ya sanar da yin hakan a karon farko, a ranar 4 ga watan Fabarairun bana. (Zainab)